Untitled Document
Mujallar Tsarin Duniya da Muhalli
Maƙálolin da aka buga (2017/2018/2019/2020/2021/2022)
Mujallar Tsarin Duniya da MuhalliEarth Systems and Environment (ESEV)tana fitar da sakamakon nazarori da bincike na asali a fannoni mabambanta wanda suke da dangantaka da ilmin kimiyyan ƙasa da muhalli wanda sa’anni suka yi bitan su. Springer da Jami’an Sarki Abdulaziz (KAU) da ke ƙasar Saudiyya suke tarayya wajen buga wannan mujallar. Mujallar ta na zaɓan nazarorin da suke ba da gudumawa wajen mu fahimce tsari da halin bangarori mabambanta na duniya da suke hulda da juna (Kaman sararin sama, teku, dukannin ƙanƙara da yake doran ƙasa, ƙasa, dukkannin ruwan da yake doran ƙasa, da sauran su). Ana ba da karfafawa da girmamawa na musamman zuwa ga nazarori a kan matakan hallitar duniya da na biogeochemical da ke jagorantan yanayi da sauyin yanayi. Ita mujallar ESEV tana cikin fihirisa na SCOPUS (Makin ambato 2019=2.0, Makin Ambato 2020=3.7, da Makin Ambato 2021=7.1). Kuma tana cikin fihirisa na ESCI (Emerging Sources Citation Index) wanda take tsammanin samun makin tasiri na farko a cikin shekaran 2021.
Batutuwa
Nazarorin da ake bugawa sun ƙunshe batutuwa na kimiyya masu fadi. An kasafta su kaman haka:
Ƙasashe
Dayawa daga cikin nazarorin da aka fitar da suke da dangantaka da wani yankin duniya ko wani ƙasa an kasafta su a bisa “Ƙasa”, kuma za a iya isa zuwa garesu a ƙarƙashin nan:
Mujalladai da Fitowa
Mujallar ESEV ta fito da nazorori a 2017, 2018, 2019, 2020, 2021 da 2022 waddan da suke da dangantaka da kimiyyan tsarin duniya da muhalli. Za a iya samun su ta wadannan shafufuka na yanan gizo:
Fitowa na Musamman:
Mujallar ta kuma buga Fitowa na musamman a shekaran 2018 wanda yake da dangantaka da Kimiyyan yanayi, Kimiyya da ruwa, Ilimin noma da tsaron abinci, Tasiri da karbuwa, Ragi da Manufofi ma Ƙasar Pakistan. Za a iya samun maƙálolin da gabatarwan a nan (Fitowa na musamman).
Dokoki masu alaƙa da ƙaddamar da nazari na bincike
Wannan mujallar tana marhaba da gudumuwar masu bincike na kimiyya a fadin duniya. Yanke shawaran karban gudumuwa domin a buga yana da alaƙa da dacewan maudu’in da aka yi rubutu akai da manufar wannan mujallar, da kuma asalin wannan gudumuwan, kuma ya zamanto abin yabo ne a kimiyyance.
Manajan Gyararraki
Za a iya ganin bayanai akan kwamitin gyararraki da kuma batutuwa na wannan mujallar ta wannan shafin:
https://www.springer.com/journal/41748/editors?detailsPage=pltci_3138733
Masu nazari da bincike zasu iya ƙaddamar da maƙalan su ta wannan shafin:
https://www.editorialmanager.com/esev/default.aspx
Don Allah, kayi rajista a kan shafin ESEV ta zaɓin “Yi Rajista a Yanzu” idan wannan shine karon ka na farko na ƙaddamar da maƙalan a wannan mujallar.
Dokoki da darusa domin amfanin Mawallafan nazorori
Za a iya samun bayanai da darusa a kan hanyoyin da ake bi wajen ƙaddamar da nazari a wadannan shafufukan.
|